A yayin wani taron gangamin da ya gudana a ranar Lahadi, jam'iyyar adawa ta MLC, ta yi kiran 'yan kasar Congo da su tashi tsaye su yi yaki da duk wani shirin kawo gyaran fuska ga dokar zabe, da kuma duk wani yunkurin da zai kawo illa ga tsarin demokaradiyya a kasar DRC-Congo. Ana son a canja dokar zabe, wannan abu ne da ba za mu amincewa da shi ba. Wannan shi ne neman kashe demokaradiyya. Ina kiran al'ummar kasar baki daya a karkashin lemar jam'iyyar MLC da su dauki nauyin dake wuyansu, domin mu wakilansu a zauren majalisar dokoki, a halin yanzu mun kasa fahimtar da abokanmu masu rinjaye a majalisar dokoki cewa kadda a kashe demokaradiyya, in ji sakatariyar jam'iyyar MLC, madam Eve Bazaiba. (Maman Ada)