in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da matakin IS na hallaka 'dan Japan
2015-01-26 10:21:59 cri

Kamitin tsaro na MDD ya yi kakkausar suka a game da kisan gillan da ake ganin kungiyar Islama ta IS ta aiwatar a kan Haruna Yukawa wani mutumin kasar Japan.

Kwamitin wanda ya bayyana damuwarsa a cikin wata sanarwa, ya kuma bukaci kungiyar ta IS da ta hanzarta sallamo Kenji Coto, wanda shi ma 'dan kasar ta Japan ne da yayan kungiyar ISIS ta kama ta rike.

Mambobin kwamitin tsaron na MDD sun jaddada cewar, wadanda ke da alhakin kashe Haruna Yukawa za'a kama su da laifin aikata kisan kai.

Kwamitin tsaron MDD ya bukaci dukanin kasashe dake karkashin kwamitin da su hada kaida kasar Japan da sauran hukumomin da suka dace kamar yadda dokokin duniya suka tanada.

Wani hoton bidiyo da kungiyar Islama ta IS ta gabatar ya nuna cewar, ankashe Haruna Yukawa wanda 'yan kungiyar Islamar suka yi garkuwa da shi.

Kuma tun farko sai da 'yan kungiyar Islamar suka bukaci gwamnatin Japan da ta ba su dalar Amurka miliyan 200 a cikin awowi 72 kafin ta saki mutanen biyu 'yan kasar ta Japan.

To amma daga baya sai 'yayan kungiyar ta IS suka kashe Haruna Yukawa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China