Hukumar sojojin kasar Najeriya ta jaddada a ranar Talata a birnin Abuja niyyarta ta kawar da kungiyar Boko Haram a cikin wannan kasa dake yammacin nahiyar Afrika.
Babban mashal na sojojin sama kuma shugaban rundunar sojojin kasar, Alex Badeh, ya yi wannan sanarwa ga manema labarai bayan wata ganawa tare da shugabannin ma'aikatar, gwamnoni da mambobin majalisar jihar Borno, Yobe da Adamawa domin tattauna kalubalolin tsaro a shiyyar. Mista Badeh ya jaddada cewa, rundunar sojojin Najeriya za ta jure wahalhalu da kalubalen da masu tada kayar baya suke kawo wannan kasa. Haka kuma ya jaddada wajabcin hadin gwiwa tare da hukumomin tsaro na kasashen Chadi, Nijar da Kamaru domin sanin ayyukan wadannan mayaka. (Maman Ada)