Sojojin Nigeriya sun ce, sun samu nasarar murkushe wani harin ta'addanci da kungiyar Boko Haram ta yi shirin kaiwa a garin Biu na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.
Yan ta'addan su biyar da bindigogin harbar jiragen sama biyu aka damke, sannan 'yan gari kuma suka fafutuki sauran maharani da suka tsere, in ji cibiyar tsaron kasar cikin wata sanarwa da ta fitar wa manema labarai.
Sojojin na Nigeriya sun yi arangama matukar gaske da 'yan ta'addan kafin su samu nasarar sake kwato yankin arewa maso gabashin Nigeriya, musamman jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe wadanda su ne wannan masifa ta Boko Haram ta fi addaba.
Boko Haram dai ta kwace garin Baga a jihar ta Borno a ranar 3 ga wannan watan, cikin harin ta na baya bayan nan inda suka yi wa mutanen garin sama da 2,000 kisan kiyashi, kamar yadda kafofin yada labarai suka tabbatar.
Sai dai kuma sojojin Nigeriya sun karyata suna mai cewa, mutane 150 ne kawai harin ya rutsa da su. (Fatimah)