in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta yi tir da kaiwa tawagar yakin neman zaben ta hari
2015-01-22 09:38:22 cri

A Najeriya jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, ta bayyana rashin jin dadi, game da yadda wasu 'yan adawa, suka afkawa tawagar neman zaben shugaban kasa, yayin gangamin kamfe da tawagar ta gudanar a jihar Katsina.

A cewar kakakin jam'iyyar Olisa Metuh, hakan ya nuna burin babbar jam'iyyar adawar kasar APC, na kokarin amshe mulki da karfin tuwo, duk kuwa da cewa an rattaba hannu kan yarjejeniyar tabbatar da sulhu tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar.

Metuh ya ce, jam'iyyarsa ba za ta amince da irin wannan cin zarafi ga 'ya'yanta ba.

Kakakin PDPn ya ce, bai kamata yayin da sauran jam'iyyu ke kara azama wajen neman amincewar al'ummar kasar, a hannu guda magoya bayan APC su mai da hankulansu ga tada husuma ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China