Tawagar jami'an sa ido ta kungiyar tarayyar Turai EU, za ta isa Najeriya nan gaba kadan cikin wannan mako, domin nazartar yadda babban zaben kasar na watan gobe zai wakana.
Wata sanarwa da ofishin kungiyar ta EU dake Najeriya ya fitar, ta ce, mamba a hukumar gudanarwar kungiyar Santiago Fisas Ayxela ne zai jagoranci tawagar, wadda kuma za ta gudanar da ayyukanta bisa tanadin dokokin kasa da kasa.
Ana kuma sa ran wakilan za su yi aiki kafada da kafada da wakilan gwamnatin Najeriyar a ranekun zabe.
Tuni dai hukumar gudanar da zaben kasar mai zaman kanta INEC, ta sanar da ranar 14 ga watan Fabarairu, a matsayin ranar zaben shugaban kasa da 'yan majalissun tarayyar kasar, yayin da zaben gwamnoni da na 'yan majalissar jihohi zai biyo baya a ranar 28 ga watan na Fabarairu.
Sanarwar ta kara da cewa, burin EU ne, ta ga an gudanar da zabukan Najeriyar bisa gaskiya da adalci, kana ayyukan wakilan sa idon za su hada da nazartar daukacin sassan zaben, ciki hadda korafe-korafen daka iya biyo bayan kammalar zabukan. Baya ga duba batun katunan zabe, da rajistar masu kada kuri'u, da ma yadda zaben ya gudana baki daya. (Saminu)