MDD ta kara nananta kiran da ta yi na kaucewa bata lokaci a wajen kwance damarar sa kai ta rundunar 'yan tawaye ta "Democratic Forces for the Liberation of Rwanda" wadanda a yanzu suke a jamhuriyar damokradiyyar Congo.
Kwamitin tsaron MDD mai mambobi 15 ya ce, bai kamata ba a samu jinkiri a wajen kwance damarar 'yan tawaye domin da ma yankin gabashin Afrika shi ne ya tsaida ranar da za'a kwance damarar dakarun na Rwanda nan da zuwa 2 ga watan Janairun shekarar badi.
Kwamitin tsaron ya fito karara ya bukaci da a dauki mataki na soji a kan 'yan tawayen wadanda suka yi taurin kai a wajen kwance damarar.
Yan tawayen wadanda yawancinsu 'yan kabilar Hutu ne sun tsallako daga kasarsu zuwa Congo bayan kisan kare dangin da aka yi a kasar ta Rwanda a shekarar 1994, kuma 'yan tawayen sun yi shela a watan Mayu a kan cewa, za su kwance damarar, daga nan sai gwamnatin damokradiyyaar Congo ta kebe ranar 9 ga watan Yuni domin kwance damarar saboda karancin wadanda suka mika wuya a wajen kwance damarar, sai kasashen Afrika a watan Yuli suka amince da a kara msu tsawon lokacin watanni shida na aje makamansu gefe guda, tare da kwance damartarsu ta soji. (Suwaiba)