Wani sabon rahoto na babban bankin duniya ya nuna cewa, kasashen kudu da hamadar Saharar Afirka, sun samu karuwar tattalin arziki da kaso 4.5 a bara, sama da kaso 4.2 da suka samu a shekarar 2013.
Rahoton ya alakanta matsakaicin ci gaban da kasashen suka samu, da karin jari da aka zuba a fannonin gine-ginen ababen more rayuwa, da bunkasar samar da amfanin gona, da kuma ci gaban da aka samu a fannin ba da hidima.
Sai dai duk da wannan ci gaba, rahoton na bankin duniya ya ce, jarin da kasashen ke samu daga ketare ya ragu a shekarar 2014, wanda hakan ya haifar da koma baya ga kasuwani masu tasowa.
Kaza lika rahoton ya bayyana cewa, a Ghana, hauhawar farashin kayayyaki, da kari kan kudin ruwa, ya yi tasiri ga masu sayayya, da masu san zuba jari, wanda hakan ya sabbaba raguwar harkokin tattalin arzikin kasar.
A Najeriya kuwa, rahoton ya yi hasashen cewa, rage darajar kudin kasar, zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki, ya kuma rage bunkasar tattalin arziki a bana, ko da yake fadada harkokin ba da hidima ka iya sanya kaimi ga ci gaban arzikin kasar cikin shekarar 2016.
A daya hannun kuma, kasar Afirka ta Kudu za ta ci gaba da samun matsakaicin ci gaban tattalin arziki, sakamakon dalilai da suka hada da karuwar hajojin da take fitarwa, da ingantar fannin makamashi.
Bisa jimilla dai rahoton ya yi hasashen dorewar ci gaban alkaluman GDP na kasashen wannan yanki da kaso 4.6 a bana, adadin da zai daga zuwa kaso 5.1 nan da shekarar 2017, bisa ci gaban da ake samu a fannonin bunkasa samar da ababen more rayuwa, da habakar noma, da kuma ingantar harkokin ba da hidima. (Saminu)