in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwan Ghana sun cafke wasu 'yan fashin teku 8
2015-01-19 09:30:35 cri

Sojojin ruwan kasar Ghana sun cafke 'yan fashin teku guda takwas a cikin ruwan kasar Ghana a ranar Asabar, in ji wata sanarwar rundunar sojojin kasar a ranar Lahadi. 'Yan fashin tekun dai an cafke su ne bayan sun rike wani jirgin ruwan dakon man fetur mai sunan MT Mariam a cikin ruwan kasar Najeriya tare da canja hanyarsa zuwa cikin ruwan kasar Ghana.

Sojojinmu dake sintirin a yankin ruwan teku sun samu labari kan wannan lamari, kuma cikin gaggauta suka isa wannan wurin domin cafke 'yan fashin tekun, in ji laftanal kanal Eric Aggrey Quashie, darektan harkokin hulda da jama'a na rundunar sojojin kasar Ghana. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China