in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu kyaututukan sallar krismati bisa aljihun gwamnati a Ghana
2014-12-10 10:18:08 cri

Gwamnatin kasar Ghana ta bayyana a ranar Talata cewa, tana kan bakanta na hana yin amfani da kudin kasa domin samar da kyaututukan sallar krismati ga mutane, kamfanoni ko kuma hukumomi.

Shugaban kasar Ghana, John Mahama ya fitar a shekarar da ta gabata da wata wasikar ba da umurni zuwa ma'aikatun gwamnati na hana amfani da kudin kasa domin sayan kayayyakin kyauta a albarkacin sallar krismati da sallar sabuwar shekara.

Wata sanarwar ministan watsa labaran kasar, Edward Omane Boamah, ya nuna cewa, umurnin na shekarar 2013 da ake amfani da shi ga dukkan ma'aikatun gwamnati dake samun kudi daga bitalmalin kasa har yanzu yana aiki, kuma dole dukkan mutanen da abin ya sha su girmama shi, in ji minista Omane Boamah. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China