in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabuwar wakiliyar MDD a Ghana ta yi alkawarin yin aiki tukuru
2015-01-16 14:22:13 cri

Sabuwar mai gudanar da ayyukan MDD a Ghana Madam Christine Evans-Klock ta yi alkawarin yin aiki wurjanjan domin tallafawa muradun ci gaba na jama'a da gwamnatin kasar Ghana.

Sabuwar wakiliyar MDD ta bayyana hakan ne a yayin da ta gana da ministar harkokin wajen kasar Ghana Hanna Serwah Tetteh, kamar dai yadda wata sanarwa ta MDD ta bayyana a can Ghana, a taron nasu, sun samu tattaunawa kan cutar Ebola da matakan da duniya ta dauka domin tunkararr lamarin.

Madam Evan Klock wacce ita ce sabuwar wakiliyar ofishin Ghana na gudanar da ayyukan raya kasashe na MDD UNDP, an nada ta kwanan nan a matsayin mai gudanar da ayyukan MDD a kasar Ghana, inda ta maye gurbin Ruby Sandhu-Rojon.

Ministar harkokin wajen Ghana da hadin kan yankuna Hanna Serwah Teteh ta ce, gwamnatin Ghana za ta baiwa sabuwar wakiliyar MDD goyon baya domin cimma muradun ayyukan MDD. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China