Dan takarar mukamin shugaban kasa bangaren babbar jam'iyyar adawa ta Nigeria APC Janar Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawar da matsalolin da suka addabi tattalin arzikin Nigeria, idan aka zabe shi a zaben shugaban kasa na 14 ga watan Fabrairu mai zuwa.
A yayin da yake jawabi a wani babban taron jam'iyyar da aka shirya a Minna a jihar Niger dake tsakiyar arewacin Nigeria, janar Buhari ya ce, zai yi amfani da dimbin albarkatun da Allah ya yi wa Nigeria a matsayin ginshiki na magance matsalolin da suka addabi Nigeria.
Buhari tare da mataimakin shi Yemi Osinbajo na daga cikin jerin 'yan takarar 11 da mataimakan su wadanda hukumar zabe mai zaman kanta ta amince da shiga takarar su a babban zaben da za'a yi a Nigeria a watan Fabarairu. Sauran wadanda hukumar zaben ta amince da takarar su sun hada da shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo, wadanda za su tsaya takarar mukamin shugaban kasa a karkashin jam'iyyar dake rike da mulkin kasar ta PDP.
A cikin jawabinsa, 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta APC Muhammadu Buhari ya kuma bayyana cewar, idan har aka zabe shi zai yi maganin matsalar tsaro, tare da dakile cin hanci da rashawa da kuma samar da ayyukan yi ga matasan Nigeria ta hanyar kirkiro da sabbin masana'antu da kuma farfado da wadanda suka daina aiki.
Daga cikin wadanda za su tsaya takarar shugabancin kasar ta Nigeria Jonathan da Buhari ne kawai suka taka rawa a zaben shekarar 2011. (Suwaiba)