Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya bayyana cewa, shugabannin kasashen yammacin Afrika sun dauki nagartattun matakai domin tabbatar da zabuka cikin lumana a Najeriya a cikin wata mai zuwa, in ji kafofin kasar a ranar Litinin.
A yayin wani taron manema labarai a birnin Accra a makon da ya gabata, mista Mahama, kuma shugaban kungiyar ECOWAS a wannan karo, ya bayyana cewa, duk da karuwar hare-haren kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, zaben shugaban kasa na ranar 14 ga watan Febrairu a cikin wannan kasa zai gudana a ranar da aka tsai da. Kasar Najeriya ba za ta iyar dage wadannan zabuka ba dalilin Boko Haram. Yin hakan zai iyar baiwa Boko Haram wata nasarar da ba ta dace da ita ba, in ji shugaban kungiyar ECOWAS.
Haka kuma mista Mahama ya nuna cewa, kungiyar ECOWAS na tuntubar hukumomin Najeriya ko da yaushe da hukumar zabe domin samun tabbacin cewa, zabukan za su kasance cikin nasara, tare kuma da bayyana cewa, kungiyoyin sa ido kan zabuka na kasa da kasa za su sa ido kan zabukan Najeriya. (Maman Ada)