Rahotanni daga Bujumbura, babban birnin kasar Burundi sun nuna cewa, an kashe 'yan bindiga 8 yayin da soja 1 ya jikkata lokacin wata arangama tsakanin sojojin kasar ta Burundi da wata kungiyar 'yan bindiga da ba'a tantance su ba, wadanda suka tsallako cikin kasar daga jamhuriyar demikradiya ta Kongo DRC.
Kamar yadda kakakin rundunar sojin kasar ta Burundi kanar Gaspard Baratuza ya shaida wa Xinhua ta wayar tarho, a safiyar ranar Talatan nan ne 'yan bindigar suka tsallako rafin Rusizi daga jamhuriyar demokradiya ta Kongo.
Ya bayyana cewa, bayan tsallokwar su, 'yan bindigar suna shirin shiga Burundi ta Bambo, wani yanki a Murwi dake gundumar Cibitoke, mai tazarar kilomita 95 daga arewa maso yammacin Bujumbura.
Kanal Baratuza ya tabbatar da cewa, sojojin Burundi ba su tabbatar da su wane ne wadannan 'yan bindigar ba, amma kuma suna zaune a kan shirin ko ta kwana a Bambo, inda 'yan bindigar suka fara shigowa. (Fatimah)