Rundunar sojojin kasar Burundi ta ce, mutane 99 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu, bayan dauki-ba-dadin da sojojin Burundin suka kwashe kwanaki 4 suna kafsawa, da wasu mahara a lardin Cibitoke, dake kusa da kan iyakar kasar da janhuriyar demokaradiyyar Congo DRC.
A cewar mai magana da yawun rundunar Kanar Gaspard Baratuza, sojojin Burundin sun hallaka mahara 95, ko da yake ya ce, akwai wasu sojoji biyu, da fararen hula biyu, da su ma suka rasu yayin bata-kashin.
Fada ya barke tsakanin bangarorin biyu ne dai tun daga ranar Talatar makon jiya, lokacin da gungun maharan da ba a tantance da ko su waye ba, suka yi yunkurin kutsawa dajin Kibira na kasar ta Burundi.
Rungunar sojin Burundin ta kuma ce, yawan maharan ya kai mutane 120 zuwa 180, akwai kuma mutane 9 da aka cafke daga cikin su, wadanda suka ki bayyana sunan kungiyar da suke wakilta ko shugaban ta. (Saminu)