Hukumar zabe ta Nigeria mai zaman kanta INEC ta kara jaddada cewar, za ta gudanar da karbabben zabe a watan Fabrairu mai zuwa ba tare da nuna wani bambamci ba.
Shugaban hukumar zaben Nigeria Attahiru Jega ya bayar da wannan tabbacin ne a cikin wata kasida da ya gabata a jami'ar Bayero dake birnin Kanon.
Jega ya ce, a halin da ake ciki ana ci gaba da kokari na kammala shirye-shirye na gudannar da zaben domin tabbatar da cewar, an gudanar da zaben kamar yadda dokokin zaben kasar suka zayyana.
Jega ya yi kira a kan masu ruwa da tsaki a game da zaben da su bayar da gudumuwar da ta dace domin tabbatar da cewar, an gudanar da zaben a bisa turbar gaskiya da lumana.
Hukumar zaben ta Nigeria ta kebe ranar 14 ga watan Fabrairu, domin gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar. Hukumar zaben ta kuma kebe ranar 28 ga watan Fabrairu mai zuwa domin gudanar da zaben gwamnoni a Nigeria. (Suwaiba)