in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya da Sin sun shirya taro game da warware rigingimu
2013-11-15 10:17:32 cri

A ranar Alhamis ne, kasashen Najeriya da Sin suka shirya wani taro a Abuja, babban birnin kasar ta Najeriya game da hanyoyin warware rigingimu, da nufin magance batutuwa da suka shafi harkokin duniya, zaman lafiya da tsaro, hadin gwiwar Sin da Afirka da sauran batutuwa.

Cibiyar bunkasa zaman lafiya da sasanta rigingimu ta Najeriya (IPCR) tare da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin da ke Najeriya ne suka shirya taron, bisa imanin cewa, lokaci ya yi kana ya zama wajibi a tattauna matakan sasanta rigingimu na gargajiya da aka saba yi.

A jawabinsa na bude taron, babban darektan cibiyar ta IPCR, Joseph Golwa, ya bayyana muhimmancin taron ga sassan biyu ta fannoni daban-daban, baya ga kasancewarsa taron kasa da kasa na biyu da cibiyar ta shirya tare da hadin gwiwar kasar Sin da nufin cimma manufa guda na samar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Ya ce, taron farko da cibiyar ta shirya a watan Nuwamban shekarar 2011, ya baiwa 'yan Najeriya damar koyon wasu abubuwa tare da musayar ra'ayoyi da Sinawa.

Darektan cibiyar ya kuma yabawa ofishin jakadancin kasar Sin, bisa ga rawar da ya taka wajen yayata wannan taro, matakan da ke nunawa a zahiri irin gagarumin rawar da gwamnatin kasar Sin ke takawa a kokarin samar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Shi ma a jawabinsa, jakadan kasar Sin da ke Najeriya, Deng Boqing, ya yaba da yabon da aka yiwa gwamnatin kasar Sin, yana mai cewa, al'ummar Sinawa na dora muhimmanci sosai ga ci gaban tattalin arzikin da inganta rayuwar jama'ar kasa ta hanyar zaman lafiya da jituwa.

Ya kuma yi kira ga kasashen duniya, da su mutunta muradu da zabin kasashen Afirka ta hanyar kaucewa tsoma baki a cikin harkokinsu na cikin gida, ba su goyon baya a kokarin da suke yi na bunkasa kansu bisa tsarinsu, mutunta manufofin nuna daidaito, tare da taimakawa al'ummar nahiyar Afirka a kokarin da suke na warware matsalolinsu da kansu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China