Ministan harkokin wasanni da motsa jiki na Nigeria Tamuno Danagogo ya yi kira a kan shugabannin gudanar da harkokin kwallon kafa a Nigeria da su yi sulhu da juna, kuma su kaucewa duk wani mataki da zai kawo cikas ga harkar kwallon kafa a Nigeria domin a samu ci gaba.
Ministan na jawabi ne a wani dandalin babban taro na musamman na kungiyar kwallon kafa ta Nigeria NFA wanda aka yi a Warri dake Delta, wadda ke kudancin Nigeria.
Ministan ya ci gaba da cewar, wasan kwallon kafa, wani abu ne dake hada kawunan 'yan kasa, saboda haka ya kamata a dauki mataki na kare wasan daga samun koma baya.
Danagogo ya yi amana a bisa cewar an samu ci gaba a harkar kwallon kafa a Nigeria, to amma ya ce, dole su shugabannin masu gudanar da harkokin kwallon kafa a ko ina a Nigeria su hada kawunansu domin a samu ci gaba mai ma'ana.
Ita dai kungiyar kwallon kafar ta Nigeria ta shiga wani hali na rikici, tun daga watan Yuli, a yayin da hukumar kwallon kafa ta duniya ta dakatar da kasar daga taka rawa a wasasnni na duniya saboda abin da ta kira katsalandan daga gwamnatin ta Nigeria a wajen tafiyar da wasan kwallon kafa, to amma daga baya an dage takunkumin shiga wasanni na duniya da aka gindayawa Nigeriar. (Suwaiba)