in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana za ta neman zama masaukin baki na gasar cin kofin Afrika ta 2017
2014-08-27 10:33:24 cri

Ministan matasa da wasanni na kasar ta Ghana, Mahama Ayariga wanda ya yi magana ta kafar shafin sadarwa na internet Twitter ya tabbatar da sha'awar Ghana ta shiga sahun kasashe masu neman zama masaukin gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2017.

Tun farko dai kasar Libya ce, aka baiwa damar ta zamanto mai masaukin bakin wasan, to amma sai Libyar ta janye saboda halin rashin tabbas da matsalar tsaro da kasar ta shiga.

Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta baiwa kasashen Afrika damar shigar da takardar sha'awar zama masaukin wasa, nan da zuwa 30 ga watan Satumba na shekara ta 2014, kuma a shekara ta 2015 ne hukumar kwallon kafar ta Afrika za ta bayyana kasar da aka zaba ta zamanto mai masaukin gasar cin kofin na Afrika.

Ita kasar Ghana da ma ta taba zamantowa masaukin gasar cin kofin Afrika a shekarar 2008, idan ta sami nasara aka zabe ta, za ta zamanto masaukin gasar cin kofin Afrika mafi girma a karo na biyu a cikin shekaru 9. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China