Mataimakin shugaban kasar Iraki Nouri Al-Maliki dake ziyarar aiki a kasar Lebanon ya yi kira a ranar Talata da kafa wata gamayyar kasashen Larabawa domin yaki da barazanar kungiyar IS.
Mista Al-Maliki da tawagar dake rakiyarsa sun gana da shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri, inda bangarorin biyu suka mai da hankali kan sabbin cigaban da aka samu na baya bayan nan a shiyyar, da barazanar ta'addanci da ta zama ruwan dare.
Ra'ayoyinsu sun zo daya kan wajabcin kare kasar Iraki, da ma shiyyar baki daya daga barazanar ta'addanci da kuma mai da hankali wajen yin hadin gwiwa domin fuskantar wannan barazana, in ji mista Al-Maliki. Mun yi imanin cewa, al'ummomi da gwamnatocin shiyyar gaba daya za su iyar murkushe kungiyar IS, in ji mista Al-Maliki bayan wata ganawarsa tare da shugaban kungiyar Hezbollah, Sayyed Hassan Nasrallah a ranar Litinin da yamma.
A cewar sanarwar Hezbollah, mutanen biyu mista Nasrallah da Al-Maliki sun bayyana imaninsu bisa nasarar al'ummomi da gwamnatocin shiyyar kan kungiyar IS, da ma wasu kungiyoyi makamantan haka. (Maman Ada)