Sojojin kasar Kamaru sun kashe mayakan Boko Haram su 116 a cikin makon nan lokacin da mayakan suka kai hari a kan sansanin sojojin a yankin arewacin kasar na Amchide, kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar ta tabbatar.
Ma'aikatar ta ba da labarin cewa, sojojinta sun samu galaba a kan mayakan kungiyar kusan su 3,000 da ake da tabbacin mambobin kungiyar na Nigeriya ne, abin da ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Kamaru uku.
Majiyar ma'aikatar tsaron da ta nemi a sakaya sunanta ta yi bayanin cewa, bangarorin biyu sun yi musayar wuta da manyan makamai a Amchide da Limani, wurare biyu dake da nisa daga arewacin kasar mai iyaka da Nigeriya, inda 'yan kungiyar ke yawan kai hare-hare.
A cewar majiyar, sojoji ukun kasar Kamarun da aka kashe suna tare da rundunar daukan matakan gaggawa ne da aka jibge su a yankin watannin baya domin kare hare-hare daga 'yan kungiyar.
An kuma ba da labarin cewa, akwai wadansu sojojin 6 da suka ji rauni. (Fatimah)