in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar Ghana za ta halarci babban taron shekara shekara na bankin duniya a Washington
2014-10-10 10:50:01 cri

Ministan kudi na kasar Ghana Seth Emmanuel Terkper zai jagoranci tawagar kasar zuwa babban taro na shekara shekara da bankin duniya da asusun ba da lamunin duniya IMF su kan yi a birnin Washington na kasar Amurka, za'a fara taron na bana yau Jumma'a 10 zuwa Lahadi 12 ga wata.

A cikin wata sanarwa da aka fitar jiya Alhamis, an ce, tawagar ta kunshi gwamnan babban bankin kasar Henry Kofi Wampah, da kuma tsohon ministan kudin kasar a zamanin mulkin Jerry John Rawlings, Kwesi Botchwey wanda a yanzu haka shi ne shugaban hukumar tsare-tsare da cigaban kasar.

A yadda sanarwa ta yi bayani, tawagar za ta kuma halarci taron ministocin kudi na kasashen renon Ingila wanda za'a yi kafin taron bankin duniya da na asusun ba da lamuni na duniya.

Kasar Ghana dai tana tattaunawa da asusun ba da lamunin duniya IMF game da hanyoyin da za ta samu domin ta fita daga halin tattalin arzikin da take ciki tare da tawagar cibiyar Breton Wood da suka riga suka ziyarci kasar ta Ghana domin fara tattaunawa.

Sanarwar da asusun ba da lamuni na duniya ya fitar har ila yau ta yi bayanin cewa, bayan tattaunawar share fage da tawagar ta yi, alamu na nuna cewa, za'a cigaba da tattaunawar lokacin babban taron nata na shekara shekara.

Gwamnatin kasar Ghana dai ta nuna alamun cewa, shirin samar da kudin da take kokarin ganin nasararsa a kasar, mai yiwuwa ne za a fara shi a farkon watan Janairun shekara mai kamawa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China