Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Chris Olukolade ya bayyana cewa, dakarun kasar sun yi nasarar kame wani 'dan kungiyar Boko Haram da ke zaton shi ne ya kaddamar da harin kunar baken waken nan na tashar motar garin Gombe da ya halaka kimanin mutane 20.
Jami'in ya ce, an yi nasasar kama wanda ake zargin ne a shingen duba ababan hawa a yankin Bajoga da ke jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya, lokacin da ya ke kokarin tserewa a cikin wata mota kirar Honda makare da abubuwan fashewa.
A wani labarin kuma, jami'an tsaro a Najeriya sun mamaye wani maboyar 'yan ta'adda a garin Kano da ke arewa maso yammacin kasar, inda aka kama wasu mutane da suka kware wajen hada bama-bamai, kuma yanzu haka suna taimakawa jami'an tsaro wajen gudanar da bincike.
Jami'an sun yi imanin cewa, wannan lamari zai taimaka musu wajen samun bayanai a kokarin da suke na yaki da masu tayar da kayar baya a arewacin kasar ta Najeriya. (Ibrahim)