Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya ce, zai tura ministoci uku da za su wakilci kasar Afrika ta Kudu a taron dandalin tattalin arzikin duniya (WEF) kan nahiyar Afrika, da zai gudana a birnin Abujan Najeriya daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Mayu, in ji fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu a ranar Litinin.
Wadannan ministoci za su hada da ministan kasuwanci da masana'antu Rob Davies, ministan kudi Pravin Gordhan da kuma ministan kula da ayyukan gwamnati da harkokin gargajiya Lechesa Tsenoli, in ji kakakin fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu, Mac Maharaj a cikin wata sanarwa.
Afrika na kasancewa har kullum a zuciyarmu game da siyasar ketare. Haka kuma mun zabi a matsayin muhimmin abu na farko, ingiza dunkulewar tattalin arzikin shiyya, bunkasa ababen more rayuwa, cigaban kasuwanci tsakanin kasashen Afrika da kuma cigaban karko na nahiyar, in ji mista Zuma a cikin wata sanarwa.
WEF, wani muhimmin dandali ne wajen kara ingiza wannan tsari, musammun ma ganin cewa, yana taimaka wa Afrika kara azama tare da sauran kasashen duniya domin samun cigaba da bunkasuwar tattalin arziki, in ji Zuma. (Maman Ada)