in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tsaurara matakan tsaro a Abuja gabannin bude babban taron tattalin arzikin duniya
2014-05-07 10:32:19 cri

An tsaurara matakan tsaro a Abuja, babban birnin tarayyar Nigeriya gabannin bude taron tattalin arziki na duniya da za'a fara a Laraban nan 7 ga wata.

Sojoji, 'yan sanda da sauran jami'an tsaro masu farin kaya suna ta kai komo cikin motoci dauke da manyan makamai, sannan kuma an ajiye wassu jami'an tsaron masu farin kaya a muhimman wurare daban daban dake cikin birnin. Za'a yi taron ne cikin wani yanayi na fargaban tsaro sakamakon harin da 'yan ta'addan nan na Boko Haram suke dinga kaiwa a jere a cikin kwanakin nan.

Dukkan manyan hanyoyi da za su kai ga babban Otel din Transcorp Hilton, dandalin taron da suka hada da titin Shehu Shagari da titin Gana, an kulle su domin a rage cunkoson motoci. An kuma tsaurara matakan tsaro har ila yau a kusan kowace hanya da mahada a garin.

A babban otel din Transcorp Hilton kuwa, dandalin wannan taro da zai samu halartar manyan shugabannin kasashen duniya da wakilansu, an saka na'ura mai tantance jikin 'dan adam a bakin kofar shiga ciki, sannan akwai 'yan sanda da sojoji da sauran jami'an tsaro masu farin kaya a ciki da harabar otel din. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China