Bisa wani bayanin da MDD ta fitar cikin wani rahotonta a jiya Litini, an ce, a kalla mutane miliyan 11.4 ne a cikin kasashe 12 ko suke gudun hijira ko kuma suka rasa matsugunninsu. Rahoton na ofishin tsara ayyukan jin kai wato OCHA ya ce, rasa matsugunni ya karu da kashi 14 a cikin 100 cikin watanni 6, abin da ya sa adadin ya zama miliyan 11.4.
Ofishin na OCHA ya yi bayanin cewa, wannan adadi ya wakilci karin mutane miliyan 1.36 tun daga karshen watan Maris, wanda kafin nan ake da miliyan 10 da suka rasa matsugunni a yankin bisa ga kididdigar baya bayan nan.
Rahoton da aka fitar sau biyu a shekara game da wadanda suka rasa muhallansu ko suke gudun hijira ya ce, wadannan mutanen sun fito ne daga Burundi, gabashin jamhuriyar demokradiya ta Congo, Djibouti, Eritrea, Habasha, Kenya, Rwanda, Somaliya, Sudan ta Kudu, Tanzaniya, Sudan da kuma Uganda. (Fatimah)