Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu 'yan bindiga da ake zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne, sun hallaka wasu mutane 32 a kauyen Gumsuri dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
An ce, baya ga wadanda suka hallaka, maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutanen kimanin 185. Shaidun gani da ido sun ce, cikin wadanda 'yan bindigar suka sace hadda matan aure, da 'yan mata, da kuma yara kanana.
'Yan kato da gora da aka fi sani da civilian JTF da dama sun samu raunuka yayin da suke kokarin dakile farmakin maharan.
Wata kafa ta rundunar sojin kasar ta ce, 'yan bindigar sun farma kauyen na Gumsuri, wanda ke makwaftaka da garin Chibok ne da sayin safiya, inda suka rika jefa bama bamai cikin gidaje. Bayan sun samu nasarar tattara mutanen kauyen ne kuma suka bude wuta kan 'yan kato da gora, da kuma dagajin kauyen, kafin daga bisani su tisa keyar saura cikin motoci biyu da suka zo da su, suka kuma fice daga yankin kafin wayewar gari.
Wani wanda ya ce ya samu damar halartar inda wannan lamari ya auku, ya shaida wa majiyarmu cewa, ba a kai ga sanin faruwar lamarin na farkon mako ba sai a baya bayan nan, sakamakon nisan kauyen da birnin jihar, da kuma rashin ingancin hanyar sadarwa. (Saminu)