in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Jonathan ya bukaci hukumar zabe da ta tabbbatar da baiwa daukacin 'yan Najeriya katin zabe
2015-01-08 10:01:52 cri

Shugaba Goodluck Jonathan na tarayyar Najeriya, ya umarci hukumar gudanar da zaben kasar INEC, da ta gaggauta kammala baiwa al'ummar Najeriyar katunan zabe na din din din, gabanin babban zaben kasar dake tafe cikin watan Fabarairun dake tafe.

Shugaba Jonathan wanda ya bayyana hakan a fadar sa dake Abuja, babban birnin tarayyar kasar, ya ce, hana 'yan kasar damar kada kuri'un su saboda rashin katunan zabe abu ne da sam ba za a amince da shi ba.

Game da korafin cewa ya zuwa yanzu, wasu ma daga gwamnonin kasar ba su kai ga samun nasu katunan ba, shugaban Najeriyar ya ce, hakan alama ce dake nuna da dama daga talakawan kasar ma, ba su samu nasu katunan ba.

Daga nan sai ya alkawarta daukar dukkanin matakan da suka wajaba, don ganin cewa, dukkanin al'ummar kasar sun samu katunan nasu, nan da lokacin da za a kada kuri'u a manyan zabukan na watan gobe.

Duk dai da ikirarin da gwamnatin Najeriyar ke yi na kara inganta shirin gudanar da babban zaben kasar dake tafe, tafiyar wahainiyar da aikin raba katunan zaben ke yi, na nuna cewa da sauran rina a kaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China