Ministan makamashi na kasar Algeria Youcef Yousfi ya shawarci kasashen dake kungiyar samar da man fetur ta duniya OPEC da su dauki mataki na rage adadin man fetur din da suke hakowa saboda a samu karin farashin man fetur.
Kamfanin dillancin labarai na Algeria APS ya ce, ministan makamashin kasar yana jawabi ne a yayin wani taron manema labarai wanda aka shirya a yankin Tamanrasset dake kudancin kasar.
Kasar Algeria wadda ita ma mamba ce a cikin kungiyar OPEC, ba ta amince ba da manyan masu samar da man fetur wadanda ke cewar, OPEC kar ta dauki mataki na samun daidaito farashin man fetur a duniya, a maimakon haka sai suke ce, a bari kasuwa ta yanke hukuncin farashin na man fetur.
Ministan makamashin Algeria ya yi hasashen cewar, farashin man fetur zai tsaya tsakanin dalar Amurka 60 zuwa 70 a kan ko wace gangar man fetur a shekarar 2015, kuma dala 80 a shekarar 2016. (Suwaiba)