Hukumar 'yan sanda a kasar Uganda sun tabbatar da cewa, mutane 93 ne wadanda suka hada da jami'an tsaro guda 10, aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon rikicin kabilanci a yammacin kasar.
Mukaddashin kakakin 'yan sanda na kasar Polly Namaye a cikin wata sanarwa ya ce, rikicin da aka yi a ranar 5 ga wannan watan da sauran manyan laifuffuka a gundumomin Kasese, Ntoroko da Bundibugyo ya janyo asasar rayukan mutane 93, ban da asara ta dukiya na kwatankwacin kudin kasar miliyoyin shillings.
Babban Sifetan 'yan sandan kasar Janar Kale Kayihura tuni ya yi aiki a tsaunin Rwenzori domin kawo karshen manyan laifuffuka da ake aikatawa a wajen, sannan kuma ya tsara yadda za'a kame masu laifi da gano wassu bindigogi da suka bace.
Kusan wadanda ake zargi 122 ne da suka hada da jami'an masarautar Rwenzururu, yanzu haka ake tsare da su dangane da wannan laifi na kai hari cikin gundumomin uku. (Fatimah)