in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bidiyon azaftar da yaro ya tada hankalin al'umma a Uganda
2014-11-25 10:59:16 cri

Wani faifan bidiyo da aka dora kan yanar gizo, wanda ke nuna yadda wata 'yar aikin gida ke azabtar da wani yaro da bai wuce watanni 18 ba, ya harzuka al'umma a kasar Uganda.

Bidiyon dai mai matukar tada hankali wanda mutane sama da miliyan 12 suka kalla ta yanar gizo, ya nuna yadda wata 'yar aiki dake kula da wani yaro a wata unguwa a wajen birnin Kampala, ta rika turawa yaron abinci da cokali, wanda ya sanya shi yin amai, daga nan ne kuma 'yar aikin ta yi jifa da yaron, ta rika dukan sa, kafin kuma daga bisani a nuno ta tana taka gadon bayan sa da kafa.

Al'ummar kasar ta Uganda dai sun nuna takaicinsu game da wannan rashin tausayi, suna masu kira da a dauki tsauraran matakai kan masu aikata irin wannan laifi.

Da take karin haske game da wannan lamari, wakiliyar asusun yara ta MDD Aida Girma, ta ce, ko kadan irin wannan halayya ta azabtar da yara, ba abu ne da za a amince da shi ba.

Bisa kididdigar asusun na yara, kusan kaso 32 bisa dari na yaran dake tsakanin shekaru 6 zuwa 17 da haihuwa, na fuskantar cin zarafi ko azaftarwa a kasar ta Uganda. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China