in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shuwagabannin gabashin Afirka za su fara taro a Uganda
2013-10-25 11:00:40 cri

Shuwagabannin kasashe mambobin kungiyar bunkasa yankin gabashin Afirka ta EAC, na daf da fara wani taron lalubo karin hanyoyin bunkasa hadin kai da ciyar da yankin gaba.

Taron wanda ake fatan fara shi tun daga ranar 30 ga watan Nuwamba dake tafe a kasar Uganda, a cewar daraktan sashe na ma'aikatar lura da ayyukan kungiyar ta EAC a Uganda, Lawrence Mujuni, zai mai da hankali ne ga tattauna muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban yankin, ciki hadda gabatar da rahoton sakamakon shirin tsara daftarin kundin mulkin gamayyar kungiyar kasashen na gabashin Afirka, da ma batun korafin da mahukuntan kasar Tanzaniya suka gabatar, na mai da kasar saniyar ware da ragowar mambobin EAC suka yi.

Da yake karin haske kan hakan, Mujuni ya ce, ba laifi ba ne idan wasu daga kasashe mambobin kungiyar sun shirya wasu tsare-tsaren samar da ci gaba tsakaninsu. Wannan dai tsokaci na Mujuni na zuwa ne daidai gabar da kasashen Kenya, da Uganda da Rwanda ke ci gaba da tattaunawa tsakaninsu, ba tare da gayyatar Tanzania da Burundi ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China