in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu za ta zama mambar kungiyar EAC a 2014, in ji ministan Uganda
2013-09-10 10:46:25 cri

Kasar Sudan ta Kudu za ta kasance mambar gamayyar kasashen gabashin Afrika (EAC) a shekarar 2014, in ji ministan kasar Uganda mai kula da harkokin shiyyar gabashin Afrika Shem Bageine dake kuma shugabancin kwamitin ministocin EAC. A cewar mista Bageine, shawarwarin kan batun amincewa da Sudan ta Kudu da aka yi sun taimaka ga cimma matsaya kuma shugabannin kasashe mambobi AEC za su iyar daukar mataki a shekarar 2014.

Akwai sharuda da ya kamata a ciki kafin duk wata kasa ta samu shiga cikin wannan gamayya. Amma a dunkule dai, kasar Sudan ta Kudu ta cika yawancin ka'idoji kuma za mu duba wannan rahoto a yayin taron kwamitin ministoci sannan mu mika shi zuwa ga shugabannin kasashen kungiyar EAC domin amincewa ta karshe, in ji mista Bageine.

A cikin watan Nuwamban shekarar 2002, shugabannin kasashen gabashin Afrika suka bukaci kwamitin ministoci da ya tattauna batun shigar da kasar Sudan ta Kudu. Haka kuma jami'in ya tabbatar da cewa, shawarwarin kan batun amincewa da kasar Somaliya a cikin kungiyar EAC na cigaba da gudana kuma ana sa ran mika rahoton karshe na bincike ga kwamitin ministoci a cikin watan Agustan shekarar 2014.

Kungiyar EAC na kunshe da kasashen Kenya, Tanzania, Uganda, Ruwanda da Burundi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China