A lokacin bude taron wannan shekarar na kwamitin harkokin mata a MDD, babban magatakardar majalissar Ban Ki-moon a ranar Litinin din nan ya kiran da a kawo karshen banbancin jinsi wanda a cewar shi yana cikin burin da ake son cimmawa a shirin muradun karni da kuma sakamako mai kyau da ake nema bayan shirin a shekara ta 2015.
Mr. Ban da yake jawabi a taro karo na 58 na kwamitin harkokin mata da yanzu haka ake yi a cibiyar majalissar, ya ce, ba za a iya cimma burin martaba juna ba, har sai an samu daidaicin jinsi a ko wane bangare.
Magatakardar majalissar ya yi bayanin cewar, akwai 'yan mata da dama yanzu a makarantun gaba da firamare, amma har yanzu akwai sauran aiki wajen kawo karshen banbancin jinsi a matakai daban daban na bangaren ilimi, yana mai nuni da tazaran dake tsakanin jinsi, musamman a mazaunan karkara da kuma mutane masu fama da nakasa, asalin 'yan kasa da sauran kungiyoyi masu banbanta jinsi.
Za'a kammala wannan taron kwamitin harkokin mata na majalissar a ranar 21 ga watan nan da muke ciki. (Fatimah)