Wasu rahotanni na cewa, kungiyar ISIS mai ikirarin kafa daular musulunci a Iraqi da Syria, ta fitar da wani sabon faifan bidiyo wanda cikin sa aka nuna wani daga mayakanta na fille kan Steven Sotloff, 'dan jaridar nan Ba'amurke da tuni kungiyar ta ISIS ta yi gargadin za ta hallaka.
Sai dai a wani jawabi da ya yi ga manema labaru a fadar White House a jiya Talata, jami'in hulda da 'yan jaridu a fadar Josh Earnest, ya ce, ba zai iya tabbatar da gaskiyar aukuwar lamarin ba. Earnest ya ce, Amurka ta dauki matakai da dama na ganin an kubutar da 'dan jaridar, ana kuma sanya ido kwarai tun lokacin da ISIS din ta yi barazanar hallaka shi. (Saminu)