in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin ta bullo da sabon shirin yaki da Sida na shekarar 2015 zuwa 2017
2014-12-03 13:22:32 cri

Gwamnatin kasar Benin ta bullo da wani sabon shirin kasa na yaki da cutar kanjamau da sauran cututtukan dake yaduwa ta hanyar jima'i bisa tsawon shekarar 2015 zuwa 2017.

A cewar kwamitin kasar na yaki da cutar Sida, shirin na dogaro wajen samar da rigakafi, magunguna, ba da jinya ga kowa, tare da nuna goyon baya ga masu fama da cutar a Benin bisa girmama 'yancin dan adam. Wannan hange na cikin tsarin manufar kungiyar yaki da Sida ta MDD, na cimma burin babu wani sabon mutum dake dauke da Sida, babu wanda ya mutu sakamakon Sida, kuma babu nuna bambanci ga masu dauke da Sida nan da shekarar 2015.

Shirin kasar Benin na da burin rage fiye da kashi 30 cikin 100 na sabbin masu dauke da Sida, sannan fiye da kashi 75 cikin 100 na sabbin masu dauke da Sida wajen kananan yara dake cikin hadari, kana fiye da kashi 50 cikin 100 na yawan mutanen dake rayuwa tare da wannan cutar kafin nan da shekarar 2017.

A 'yan shekarun baya bayan nan, kasar Benin ta samu alkaluma masu kyau wajen yaki da cutar Sida, musammun ma wajen daidaita yaduwar cutar da kashi 1,2 cikin 100 tun a shekarar 2006, samar da jinya da magunguna ga mutane kimanin dubu 25 dake karbar magungunan rage kaifin cutar a cikin mutane dubu 35 dake fama da Sida da aka kiyasta cewa nuna cikin bukata nan da shekarar 2015, da kuma ba da kariya ga mutanen da suka kamu da cutar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China