Wani jirgin ruwa dake dauke da mutane ya nutse a ranar Alhamis a tafkin Tanganyika, dake gundumar Katanga dake kudu maso gabashin DRC-Congo, tare da janyo mutuwar mutane 126, in ji Top Congo, wani gidan rediyo mai zaman kansa dake birnin Kinshasa. Kuma an ceto rayukan mutane 221, a cewar wannan majiya.
Har dai zuwa yanzu, hukumomin kasar ba su ba da wani adadi ba na wannan hadarin jirgin ruwan. Hadarin dai ya faru a ranar Alhamis da yamma tsakanin biranen Moba da Kalemie, wanda ake ganin nauyin jama'a da kayayyaki da kuma iska mai karfi dake kadawa su ne dalilin abkuwar wannan hadari.
A ranar 22 ga watan Maris na baya baya, mutane fiye da 200 suka mutu a yayin da wani jirgin ruwan dake dauke da 'yan gudun hijiran DRC-Congo ya nutse a tafkin Albert, dake kan iyaka tsakanin DRC-Congo da Uganda. (Maman Ada)