Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Mali (MINUSMA) na shirya ranakun nazari kan shirin yarjejeniyar zaman lafiya da kasar Aljeriya mai shiga tsakani ta gabatar daga ranar 7 zuwa 18 ga watan Janairu a birnin Bamako, tare da halartar jami'iyyun siyasa, maza da mata 'yan kasuwa, matasa da mata, in ji wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofinta.
Shirin yarjejeniyar ya samo asili ne daga tsarin shawarwarin da aka fara a birnin Alger tun cikin watan Yulin da ya gabata tsakanin gwamnatin kasar Mali da kungiyoyin masu dauke da makamai dake arewacin kasar domin kai ga cimma sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya daga dukkan fannoni kuma ta karshe. Tunanin reshen harkokin siyasa na MINUSMA na shirya ranakun nazari na cikin tsarin ba da kwarin gwiwa ga dukkan al'ummar kasar Mali zarafin bullo da wata mafita ta kawo karshen rikicin da kasar ke fuskanta. (Maman Ada)