Fadar shugaban kasar Mali ta bayyana sunan jami'i mai shiga tsakanin gwamnati da 'yan tawayen kasar Modibo Keita, a matsayin sabon firaministan kasar.
Rahotanni daga fadar gwamnatin Malin na cewa, tuni shugaba Ibrahim Boubacar Keita, ya amince da nadin Modibo Keita, bisa tanajin kundin mulkin kasar.
Sabon firaministan dai ya maye gurbin Moussa Mara ne wanda ba da jimawa ba ya yi murabus daga mukamin sa.
A cikin watan Afirilun bara ne dai aka nada Keita matsayin babban wakilin shirin tattaunawa tsakanin sassan kasar ta Mali, ya kuma taba kasancewa firaministan kasar a shekarar 2002, a gwamnatin tsohon shugaban kasar Alpha Oumar Konare. (Saminu)