in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi tir da hare-haren ta'addanci a arewa maso gabashin Najeriya
2014-07-01 10:47:00 cri

Babban sakataren MDD ya yi allah wadai da ci gaban da ake yi da aiwatar da munanan hare-haren ta'addanci a arewa maso gabashin tarayyar Najeriya, a kan farar hula, ya jaddada cewar, MDD a shirye take ta taimakawa kasar, dake yammacin Afrika domin a murkushe kalubalen hare-haren.

Ban Ki-moon, wanda ya yi magana a cikin wata sanarwa da ta fito daga hannun kakakin shi, ya ce, yanzu hare-haren da ake kaiwa sun zama ruwan dare, idan aka yi la'akari da hare-haren da aka kai a karshen mako, a kan wasu kauyuka, da majami'u na coci, a kusa da kauyen Chibok, inda a nan ne kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata 200 'yan makarantar sakandare.

Ban ya ce, kare 'yancin dan'adam a duniya, wani abu ne da ya wajaba a kan MDD, kuma za ta taimakawa Najeriya ta dakusar da wannan matsala, ya kuma mika jajensa da goyon baya ga wadanda tashin hankalin ya rutsa da su da kuma al'ummar Najeriya baki daya. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China