in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban MDD ya yi allah wadai da harin bam da aka kai babban birnin Najeriya
2014-06-27 11:00:08 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi tir da mummunan harin bam din da aka kai kusa da wata cibiyar sayar da kayayyaki a babban birnin Najeriya Abuja.

Rahotannni sun ce, harin da aka kai ranar Laraba, ya haddasa asarar rayuka a kalla mutane 21.

Babban sakatare na MDD ya bayyana a cikin wata sanarwa cewar, yana matukar damuwa a game da karuwar tashin hankula a kasar, wacce ke Afrika ta yamma.

Ban ya mika gaisuwar ta'aziyyar shi ga iyalan wadanda harin ya shafa, tare da yiwa wadanda suka sami raunuka, fatan samun sauki a cikin gaggawa. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China