Fiye da 'yan kasar Najeriya 3000 da 'yan asilin kasar Chadi 540 suka gujewa tashe tashen hankalin kungiyar Boko Haram a Najeriya, domin samun mafaka a yakin tafkin Chadi dake makwabtaka da Najeriya, in ji faraministan kasar Chadi, Kalzeube Payimi Deubet a ranar Laraba.
Tun cikin watan Disamban shekarar 2014, an yi rika ganin yadda 'yan gudun hijirar Najeriya suke kwarar zuwa yankin tafkin Chadi, musammun ma a garin Ngouboua.
Muna fargabar wannan matsala ta janyo mana abin da ya fi karfin mu, idan ba mu dauki matakai a lokaci ba, in ji mista Kalzeube Payimi Deubet a cikin wani jawabinsa a gaban jakadun kasashen waje dake kasarsa. Domin fuskantar wannan matsala ta tsaro da jin kai, shugaban gwamnatin kasar Chadi ya sanar da cewa, kasarsa ta dauki matakan tura sojoji a wannan yankin domin tabbatar da tsaron 'yan gudun hijirar Najeriya da kuma 'yan Chadin da suka dawo, har ma da kai musu taimakon abinci da kayayyakin bukatun yau da kullum da na kiwon lafiya. An samu bullowar wasu cututtuka, lamarin da ke kara tsananta matsalar jin kai a wannan wurin, in ji mista Kalzeube tare da yin kira ga hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa domin fuskantar wannan matsala. (Maman Ada)