Ministan harkokjn waje na kasar Mali Abdoulay Diop ya yi kira a kan bangarorin da ke rikici da juna a arewacin kasar da su dauki wani mataki na samar da yarjejeniyar sulhu a cikin gaggawa a jiya Alhamis.
Diop wanda ke magana da manema labarai a karshen wani taro da ya yi da ministan harkokin waje na Algeria, Ramtane Lamamra a karkashin wata tattaunawa ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma wasu wakilan siyasa da na soji daga arewacin Mali ya ce, ya kamata su tunkari samar da zaman lafiya, tare da murkushe tashin hankalin dake addabar arewacin kasar Mali.
Za kuma a ci gaba da gudanar da tattaunawa kan batun Mali a Algiers a karo na uku a karkashin shugabancin ministan harkokin waje na Algeria Ramtane Lamamra.
Tattaunawar za ta kuma sami halarcin wakilan wasu kungiyoyi 6 da gwamnatin Mali da kuma kungiyar tattalin arziki ta Afrika ta yamma ECOWAS da kuma wakilan MDD da kungiyar kasashe musulmi da kungiyar tarayyar Turai EU da kuma kasashen Burkin Faso, Mauritania, Niger, Chadi da kuma Nigeria. (Suwaiba)