Kasashen Aljeriya da Chadi sun bayyana ra'ayi guda game da batun warware rikice rikice a kasashen Libiya da Mali, in ji shugaban kasar Chadi Idriss Deby Itno a ranar Lahadi, da yanzu haka yake ziyarar aiki a kasar Aljeriya.
Ra'ayoyin Aljeriya da na Chadi kan batutuwan da suka shafi kasashen Libya da Mali sun zo daidai, in ji mista Deby bayan ganawarsa tare da takwaransa na kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika.
Game da batun Libya, babban bakon Aljeriya ya ba da ra'ayin cewa, dukkan kasashen dake makwabtaka da Libya su yi kokarin cimma wata hanya guda domin taimaka wa wannan kasa, tare da nuna cewa, yawan hanyoyin da kasashen waje suke dauka na dakile yin shawarwari tsakanin 'yan kasar Libya.
Kan batun Mali kuma, ya jaddada goyon bayan kasarsa kan kokarin da kasar Aljeriya ke yi domin kai ga warware rikicin Mali cikin ruwan sanyi, ya kara da cewa, dukkan fatan alherin samun mafita kan wannan rikici sun rataya kan kasar Aljeriya.
A shekarar 2013 ne, kasar Faransa ta tura sojojinta zuwa kasar Mali domin yaki da masu kishin islama da suka kwace arewacin kasar, haka kuma sojojin Chadi sun shiga wannan yaki, a lokacin da kasar Aljeriya ta yi kira da a cigaba da samar da hanyoyin diplomasiyya domin warware rikicin arewacin kasar Mali. (Maman Ada)