Rahotanni daga birnin Algiers, fadar gwamnatin kasar Aljeriya, na cewa, rundunar tsaron kasar ta tsaurara matakan tsaro, domin dakile duk wani hari na ramuwar gayya, da kungiyar mayaka 'yan kishin Islama dake kasar ka iya shiryawa, sakamakon kisan shugabanta.
Hakan dai na zuwa ne bayan da rundunar sojin kasar ta sanar da hallaka madugun kungiyar mai alaka da kungiyar IS Abdelmalek Gouri.
Tuni dai aka baza jami'an tsaro a muhimman gine ginen gwamnatin kasar, da kuma wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje dake kasar, ciki hadda na kasashen Faransa, da Amurka da Birtaniya.
A cikin watan Satumbar da ya gabata ne dai kungiyar mayakan sa kan ta kasar Aljeriya, ta bayyana cewa, ta fille kan Baturan nan 'dan kasar Faransa mai suna Herve Gourdel, bayan da ta samu nasarar sace shi. (Saminu)