Dan marigayi shugaban kasar Zambiya Michael Sata ya sanar a ranar Labara cewa, ya janye daga yakin neman zaben shugaban kasa. Mulenga Sata, dake cikin jerin sunaye goma na mambobin jam'iyyar dake mulki (PF) dake neman shugabancin jam'iyyar kafin zaben shugaban kasar na watan Janairu mai zuwa, ya bayyana cewa, ya dauki niyyar janyewa bayan ya shawarci uwar rikonsa da kuma surukarsa. Ya shaida wa 'yan jarida a yayin wani taron manema labarai cewa, ba zai goya wa 'yan takara ko guda ba a zaben shugaban kasa mai zuwa, wanda daga cikinsu akwai surukarsa, madam Christine Kaseba-Sata. (Maman Ada)