in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta yi hasarar dala biliyan 6 dalilin satar man fetur bana
2014-10-23 15:00:26 cri

Tarayyar Najeriya za ta yi hasarar kimanin dalar Amurka biliyan shida dalilin satar danyen mai da kudaden shiga na mai da suka bace ba tare da wani bayani ba a karshen shekarar 2014, a cewar masu bincike a wannan fanni. Kwararrun sun bayyana cewa, wannan adadi zai iya haurawa a shekarar 2015 idan har gwamnatin Najeriya ba ta dauki kwararrun matakai ba. Mista Ben Naanen na cibiyar tarihi da harkokin diplomasiya na jami'ar Fatakwal da Patrick Tolani na cibiyar taimakon 'yan ceto dake Burtaniya suka gudanar da wannan bincike.

Rahoton ya nuna cewa, satar gurbataccen mai da lalata bututun mai, wasu hanyoyi ne na nuna adawa da cigaban hakar man fetur da rashin kula da gwamnatin Najeriya take nunawa al'ummominta bisa tsawon lokaci. Rahoton ya nuna cewa, sakaci ya tilastawa jama'a maida martani ta hanyar ayyukan lalata gine-ginen samar da man fetur idan aka yi la'akari da halin talaucin da jama'a suke ciki, alhali kuma kasarsu na da arziki.

A cewar rahoton, Najeriya na da matsayin satar mai mafi girma kuma tana daga cikin kasashe masu haduran kiwon lafiya mafi girma dake da nasaba da gurbacewar yanayi sakamakon man fetur a duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China