Gwamnatin tarayyar Nigeriya tana son sake duba hasashen da ta yi na kudin mai daga dala 77,5 zuwa dala 73 a cikin kasafin kudin shekarar mai zuwa. Ministan kudin na kasar Ngozi Okonjo-Iweala ta ce, za'a aika da bukatar hakan ga majalissar dokokin kasar, a lokacin da take bayanin ga manema labarai a Abuja.
Mrs. Okonjo-Iweala ta yi bayani game da dabarun da gwamnati ta samar dangane da faduwar darajar man a kasuwannin duniya, tana mai bayanin cewa, za'a sake nazarin hasashen matsakaicin lokacin da aka yi a da wato MTEF.
Ministan ta ce, gwamnati tana duba hanya mafi sauki da za ta tunkari halin da ake cikin yanzu, tana mai lura de cewar, hasashen da ake yi a kan man zai ci gaba da faduwa zai dauki lokaci mai tsawo nan gaba.
Ta ce, gwamnati za ta duba wassu hanyoyin da ya kamata ta bi domin tinkarar halin da ake ciki yanzu, ta yadda za ta shawo kan sakamakon da faduwar darajar man ta kawo. Daga cikin hanyoyin da za ta bi, ita ce shawarar da hukumar samar da haraji ta kasar wato FIRS ta bayar ta fadada hanyoyin da za'a samar da kudin shiga ta biyan haraji. (Fatimah)