in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gurfanar da Amurkawa 2 gaban kotu bisa zargin tallafawa yunkurin juyin mulki a Gambia
2015-01-06 09:51:32 cri

Ma'aikatar shari'ar kasar Amurka, ta bayyana sunayen wasu Amurkawa biyu da za su gurfana gaban kuliya, bisa zargin tallafawa yunkurin juyin mulki a kasar Gambia.

A cewar wata sanarwa da ofishin mai gabatar da kara Eric Holder ya fitar, Cherno Nije, da Papa Faal za su fuskanci shari'a ne, bayan da aka zarge su da shiga kasar Gambia, domin taimakawa yunkurin da aka yi na kifar da gwamnatin shugaba Yahya Jammeh a ranar Talatar makon jiya, sa'an nan suka koma Amurka bayan juyin mulkin ya ci tura.

Tuni dai aka cafke mutanen biyu bayan saukar su kasar Amurka.

Sanarwar ta ce, mutanen biyu sun kitsa aikata mummunan laifi da ya shafi wata kasa ta waje, wanda hakan ya sabawa dokar kasar Amurka, don haka ya zama wajibi su fuskanci hukuncin laifin da suka aikata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China