in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke mutane 2 a Sweden da ake zargi da kisan kiyashin Rwanda
2014-09-25 10:37:56 cri

An cafke wasu 'yan kasar Rwanda biyu a kasar Sweden bisa zargin da hannu kan kisan kiyashin Rwanda a shekarar 1994, a cewar wasu majiyoyin shari'a a birnin Kigali a ranar Laraba. Wadannan mutane biyu suna cikin jerin sunayen mutanen dake ake zargi a wannan kisan kare dangi bisa babban mataki, wadanda aka fi neme ruwa a jallo, in ji kakakin kotun shari'a Alain Mukuralinda a gaban manema labarai, amma duk da haka Mukuralinda ya bayyana cewa, har yanzu ba'a bayyana sunayen mutanen biyu ba, kana hukumomin shari'a na Sweden suna cigaba da gudanar da bincike kan matsayin da mutanen biyu suka rike a lokacin kisan kiyashi kan kabilar Tutsi a shekarar 1994.

Amma ina tabbatar maku da cewa, daya daga cikin mutanen biyu injiniya ne mai shekaru 55 da haifuwa, wanda ya taba yin aikin malamin makaranta kafin yakin basasan, kana daga baya ya dauki takardar zaman 'dan kasa ta Sweden, kana gudan 'dan kasar Rwanda ne, da ya samu takardar zama a Sweden, kuma yake cigaba da zama a wannan kasa kusan shekaru da dama, in ji wannan jami'in shari'a.

Muna fatan Sweden za ta tuso keyarsu zuwa Rwanda, ko kuma zuwa babban kotun Arusha na MDD dake kasar Tanzaniya, idan kuma hakan ba ta samu ba, to a gurfanar da su a gaban kotunan shari'a na kasar Sweden, in ji mista Mukuralinda.

Tun bayan kawo karshin kisan kiyashin a cikin watan Yulin shekarar 1994, hukumomin shari'ar kasar Rwanda suka bukaci kasashen Turai da su tuso keyar da wasu mutanen da ake zargi kan wannan lamari zuwa Rwanda domin su fuskanci shari'a, musammun ma wadanda suka samu mafaka a Turai da Amurka ta Arewa. Daga cikin wadannan kasashe, akwai Belgium, Holland, Canada, da Danmark. Amma kuma duk da haka, wasu kasashe ba su ba da hadin kai ga kokarin Rwanda domin cafke muhimman mutanen. A shekarar 2006, kasar Rwanda ta fitar da jerin mutane guda 93 da ake zargi da kisan kiyashi a Rwanda dake gudun hijira a nahiyoyin Afrika, Turai da Amurka. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China